Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mujallar "Nature" ta yi nadamar alakanta cutar COVID-19 da Wuhan
2020-04-11 20:15:37        cri
Shahararriyar mujallar "Nature" mai wallafa bayanan kimiyya ta kasar Birtaniya, ta bayyana nadamarta har karo 3, kan yadda ta alakanta cutar COVID-19 da birnin Wuhan da kasar Sin a baya.

Mujallar ta fara neman afuwa a ranar 7 ga watan Afrilu, inda ta buga wani bayani a shafinta na intanet.

Sa'an nan a ranar 8 ga watan Afrilu, mujallar "Nature" ta sake wallafa wannan bayani a shafin sada zumunta.

Daga bisani, a ranar 9 ga wata, mujallar ta fassara wannan bayani zuwa Sinanci, sa'an nan ta nuna shi a shafin sada zumunta na Wechat na kasar Sin.

Wannan bayani mai taken "Daina alakanta wani da Coronavirus" ya nuna cewa, lokacin da hukumar lafiya ta duniya WHO ta nada sunan "COVID-19" ga cutar da wata sabuwar nau'in kwayar cutar Corona ta haddasa, ta taba tunasar da wasu kungiyoyin da suka taba alakanta cutar da birnin Wuhan da kuma kasar ta Sin, ciki har da muhallar "Nature". Sa'an nan mujallar ta ce, "Abin da muka yi a lokacin baya kuskure ne, za mu dauki alhaki kuma mu nemi afuwa."

Ban da neman a yi mata afuwa, mujallar "Nature" ta ce, hukumar WHO ta taba yin sanarwa a shekarar 2015, inda ta bukaci a daina alakanta wata cuta da wani wuri, ko wata al'umma, don magance wasu munanan illoli, misali yadda ake nuna tsoro da fushi ga mutanen dake wani wuri. Cikin bayaninta, mujallar "Nature" ta ruwaito wasu masanan ilimin hana yaduwar cututtuka na cewa, yaduwar wata cuta ta kan haddasa batun shafawa wasu mutane bakin fenti. Saboda haka, kowanenmu na bukatar yin taka tsan-tsan, kar rika magana yadda muka ga dama. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China