Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Najeriya: Najeriya da Sin na kara zurfafa zumunci tsakaninsu yayin hada kai domin dakile COVID-19
2020-04-21 19:56:04        cri
A jiya 20 ga watan nan na Aflilu, darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin a tarayyar Najeriya Charles Onunaiju, ya gabatar da wani sharhi mai taken "Yunkurin dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19, da hadin kai tsakanin Najeriya da kasar Sin" a daya daga kafofin watsa labarai ta kasar wato jaridar "Blueprint", inda ya yi nuni da cewa, annobar COVID-19 wadda ta barke ba zato ba tsammani, ta kawo wa daukacin kasashen duniya kalubale, da barazana da ba a taba ganin irinsu ba a baya, don haka dole ne kasa da kasa su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, domin ganin bayanta cikin hanzari.

Charles Onunaiju ya ce har kullum kasashen Afirka da kasar Sin, suna gudanar da hadin gwiwar kiwon lafiyar jama'ar su, haka kuma kasar Sin tana samar da tallafinta ga kasashen Afirka gwargwadon karfinta, a don haka ya yi kira ga kasarsa, da ta kara darajanta huldar dake tsakaninta da kasar Sin, ta koyi fasahohin dakile annobar da kasar Sin ta samu, ta yadda za a ingiza ci gaban huldar dake tsakanin sassan biyu, yayin da suke kokarin dakile annobar tare.

A cikin sharhin, Charles Onunaiju ya bayyana cewa, tun bayan barkewar annobar a kasar Sin, nan take gwamnatin kasar ta dauki matakan da suka dace daga dukkanin fannoni, har ta cimma burin hana yaduwar annobar a fadin kasar, lamarin da ya samu yabo matuka wajen sauran kasashen duniya.

A hannu guda kuma, hukumar lafiya ta duniya ita ma ta yi kira ga sauran kasashen duniya, da su yi koyi da fasahohin kasar Sin a wannan bangaren, bayan da ta yi rangadin aiki a kasar ta Sin.

Amma a cewar sa, abun takaici shi ne wasu 'yan Najeriya kalilan dake zaune a kasar Sin, sun saba wa ka'idojin da gwamnatin kasar Sin ta tsara yayin dakile annobar, har ma sun gabatar da hotunan bidiyo ba na gaskiya ba, inda wadannan mutane suka gurgunta zumuncin dake tsakanin Najeriya da kasar Sin, lamarin da ya haifar da matukar bakin ciki.

Ya ce a halin da ake ciki yanzu, ya dace Najeriya ta kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin, domin kara fahimtar juna tsakaninsu, tare kuma da ciyar da huldar dake tsakanin sassan biyu gaba yadda ya kamata. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China