Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Aikace-aikacen kasuwanci tsakanin kasa da kasa da Sin ta yi sun farfado da tsarin samar da kayayyaki a duniya
2020-04-21 16:06:36        cri
A halin yanzu, an tsayar da wasu aikace-aikacen sayayya a wasu kasuwannin duniya, sanadiyyar yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 cikin kasa da kasa. Kamfanonin kasa da kasa, ciki har da kamfanonin kasar Sin suna dukufa wajen neman hanyoyin ci gaba, da kuma sabunta tsarin kasuwanci don habaka kasuwanni a wannan lokacin da ake fuskantar matsalar annobar. A wannan lokacin kuma, kamfanonin kasar Sin suna dukufa wajen raya harkokin kasuwanci dake tsakanin kasa da kasa, domin farfado da tsarin samar da kayayyaki na kasa da kasa.

A kwanakin baya, an dawo da tafiye-tafiyen jiragen kasa masu jigilar kayayyaki tsakanin kasar Sin da kasashen Turai. A ranar 7 ga wata, kasar Sin ta tsai da kudurin kafa yankunan gwajin kasuwanci 46 tsakanin kasa da kasa ta yanar gizo, tare da yankuna 59 da aka riga aka zartas da kafawarsu a baya, gaba daya, za a samu yankunan gwajin kasuwanci ta yanar gizo a tsakanin kasa da kasa guda 105 a fadin kasar Sin, wadanda suka shafi dukkanin birane, larduna da yankuna masu cin gashin kansu na kasar.

Lamarin da ya nuna cewa, aikace-aikacen kasuwanci dake tsakanin kasa da kasa da kasar Sin ta yi sun farfado da tsarin samar da kayayyaki na kasa da kasa. Za su kuma farfado da harkokin sayayya a kasuwannin duniya, wadanda aka dakatar da su na gajeren lokaci sanadiyyar barkewar cutar numfashi ta COVID-19. Manufofin raya tattalin arziki da gwamnatocin kasa da kasa suka gabatar ba za su amfana ba, idan ba a tafiyar da tsarin samar da kayayyaki na kasa da kasa yadda ya kamata ba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China