Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cibiyar kasuwanci ta Shanghai ta samu karin damar hada hada 22
2020-03-18 13:06:40        cri
Yankin cibiyar cinikayya ta Lujiazui dake birnin Shanghai, ya samu karin hada hadar cinikayyar cikin gida da na waje da yawan su ya kai 22 cikin wannan shekara ta bana, a gabar da ake ci gaba da yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Zhou Haidong, jami'i a kwamitin gudanarwa a yankin kasuwanci da cinikayya na Lujiazui, ya ce yankin ya karbi sabbin harkokin da suka shafi hada hadar kudi, da kula da kadarori, da samar da hidimar fito da sauran su. Ya ce ya zuwa ranar Talata, Lujiazui ya jawo lasisi 8 daga cibiyoyin kudi, da takardun gudanar da harkokin kula da kadarori na kasa da kasa 3.

Ya zuwa ranar 14 ga watan Fabarairu, duk da yaki da ake yi da cutar numfashi ta COVID-19, kamfanin Russell Investments Management na birnin Shanghai, ya kammala rajistar ba da hidimar harkokin kudi a Sin.

Shugaban kamfanin Ying Tan ya ce, Sin ce kasa mafi samar da dama da ke jawo kasuwannin waje, domin ba da hidimar lura da kadarori, don haka muka zabi birnin Shanghai. Ya ce cibiyar Lujiazui ce wurin da za su fara hada hada domin fadada harkokin kamfanin su a nan gaba.

A ranar 1 ga watan Maris na bana, birnin Shanghai ya fitar da jerin sabbin ka'idoji na bunkasa hada hadar kamfanonin waje, ciki hadda na saukaka samar da damar kasuwanci, da zurfafa bude kofa, a wani mataki na bunkasa ci gaba, da takaita mummunan tasirin da cutar COVID-19 ta haddasa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China