Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin zata ingiza shirin kyautata muhallin kasuwanci a duk fadin kasar
2019-10-29 13:04:41        cri
Mahukuntan kasar Sin sun ce gwamnati zata dauki karin matakan cigaba da inganta muhallin kasuwanci a duk fadin kasar.

Lin Nianxiu, mataimakin shugaban hukumar bunkasa cigaba da yin gyare-gyare ta kasar Sin ya bayyana a lokacin wani taron musayar kwarewa cewa, inganta yanayin muhallin kasuwanci muhimmin al'amari ne da zai kara tabbatar da bude kofar kasar ga duniya.

Cikakken tsarin kasuwanci, bisa bin doka da da oda, da samar da muhallin kasuwanci mai inganci a duniya, suna da matukar muhimmanci wajen kara kaimi ga fannonin kasuwanci, da inganta karfin gwamnati wajen tafiyar da mulki, da kuma bunkasa matsayin shirin bude kofa, a cewar jami'in na kasar Sin.

A makon da ya wuce bankin duniya ya gabatar da wani rahoto cewa, sassaucin da kasar Sin ta yi a bangaren kasuwanci ya daga matsayinta zuwa ta 31 daga matsayi na 46 a shekarar bara, inda kasar ta samu shiga cikin jerin kasashen duniya 10 mafiya inganta harkokin tattalin arzikinsu bayan aiwatar da dokokin sauye sauye.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China