Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na neman ra'ayin al'umma kan daftarin tanadin doka na jerin sunayen wandanda suka sabawa ka'idojin kasuwanci
2019-07-12 10:34:30        cri

Hukumar dake sa ido kan harkokin kasuwanci ta kasar Sin, ta fitar da daftarin tanadin doka na jerin sunayen wadanda suka sabawa ka'idojin kasuwanci da aka yi wa gyaran fuska a shafinta na website, domin jin ra'ayin al'umma.

Hukumar ta ce an fitar da daftarin ne domin inganta sa ido kan harkokin kasuwanci bisa ingantaccen tsarin samar da bashin kasuwanci.

Karkashin daftarin da aka yi wa gyaran fuska, sa ido kan harkokin kasuwanci zai shafi bangarorin da suka hada da magunguna da abinci da kayayyakin aiki na musammam, haka zalika za a kara mayar da hankali ga sauran bangarorin dake da muhimmanci ga rayuwa da lafiyar jama'a.

Daftarin zai fadada daga kan kamfanoni zuwa daidaikun 'yan kasuwa da kungiyoyin al'umma, da kuma daidaikun mutanen dake da alhakin aikata laifuka kai tsaye a kamfanonin da suka sabawa ka'idojin da sauran bangarori masu ruwa da tsaki a harkar kasuwanci.

Har ila yau, daftarin da aka yi wa gyaran fuska, ya zayyana wasu laifuka 36 da ake shawartar 'yan kasuwa da daidaikun mutane kada su aikata domin gujewa shiga cikin jerin sunayen wadanda suka saba ka'idojin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China