Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta fitar da jadawalin sassan marasa tabbas a fannin cinikayya in ji ma'aikatar kasuwancin kasar
2019-06-07 15:59:24        cri

A jiya Alhamis ne ma'aikatar kasuwancin kasar Sin, ta ce nan gaba kadan, za ta fitar da jadawalin sassan marasa tabbas a fannin cinikayya da kasar.

Ko da yake ma'aikatar ba ta yi cikakken bayani game da ranar fitar da jadawalin ba, amma kakakin ta Gao Feng, ya ce ana nazari kan wasu sassa dake rajin goyon bayan wani sashe, da wasu kamfanoni, da kungiyoyi, da wasu daidaikun mutane.

Jami'in ya yi wannan tsokaci ne yayin taron manema labarai na mako mako da ake gudanarwa, inda ya ce yayin da ake shirin fitar da jadawalin, Sin za ta lura da matakan kasa da kasa da ake aiki da su, tare da kare tsarin kasuwanni, domin ba su damar ci gaba da takara yadda ya kamata.

Mr. Gao ya kara da cewa, matakin na kasar Sin zai dakile wasu sassa dake karkata ga wani bangare, ba tare da dalilai na kasuwanci ba. Ya ce hakan ba zai shafi dukkanin sassan dake kare dokoki, kwangiloli da tsare tsaren kasuwancin kasar Sin ba.

Jami'in ya ce, yayin da ake aiwatar da matakai kan jerin sunayen wadannan sassa marasa tabbas a fannin kasuwanci, a hannu guda za a kare martabar kamfanoni dake gudanar da hada hadar su ta halak bisa doka.(Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China