2020-04-18 16:45:45 cri |
Da yake jawabi yayin wani taron manema labarai ta kafar bidiyo daga Geneva a jiya, Tedros Ghebreyesus, ya ce cikin makon da ya gabata, an samu karuwar kaso 51 na wadanda suka kamu da cutar a Afrika, yayin da aka samu karuwar kaso 60 na wadanda suka mutu a nahiyar.
Ya ce la'akari da kalubalen da ake fuskanta na samun kayayyakin gwaji, akwai yiwuwar ainihin adadin ya zarce wanda aka bayar.
A cewarsa, da taimakon WHO, yanzu galibin kasashen Afrika na iya gwajin cutar, sai dai har yanzu akwai gibi sosai na samun kayayyakin gwajin.
Har ila yau, ya ce suna aiki da abokan huldarsu wajen cike wannan gibi da kuma taimakawa kasashen Afrika yaki da cutar. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China