Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Tallafawa WHO tamkar kiyaye gamayyar bangarori daban daban
2020-04-19 16:47:08        cri
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya bayyana cewa, a wannan muhimmin lokaci da duniya ke kokarin yaki da cutar COVID-19, taimakawa hukumar lafiya ta duniya WHO tare da babban daraktan hukumar ya kasance a matsayin ceton tsarin gamayyar bangarori daban daban.

Wang, ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawa ta wayar tarho tare da babban daraktan hukumar ta WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana cewa, tallafawa hukumar tamkar ceton ayyukan MDD ne da irin ayyukan da take gudanarwa a kasa da kasa ta fuskar yaki da cututtuka.

A cewarsa, an zabi Tedros a matsayin babban daraktan hukumar WHO da gagarumin rinjayen kuri'u, kuma ya samu amincewar mambobin kasashen duniya, Wang ya ce, Tedros, shi ne shugaban WHO na farko da aka zaba daga kasashe masu tasowa, musamman daga nahiyar Afrika, kuma hakan ya kara nuna ci gaba da wayewar kan bil adama.

Tun bayan da ya kama aiki, babban daraktan ya mayar da hankali kan al'amurran da suka shafi batun lafiyar al'ummar kasa da kasa kuma yana ba da gagarumar gudunmawa wajen tafiyar da ayyukan lafiya, hakan ya sa yana samun yabo daga dukkan bangarori, in ji Wang.

Sukar lamiri da zarge zargen da ake yiwa hukumar WHO ba su da tushe balle makama, kuma matsin lambar da ake yiwa hukumar ba zai samu goyon bayan kasa da kasa ba, ya kara da cewa, babu wata kasa mai cikakken tunani da za ta goyi bayan masu kushewa hukumar ta WHO.

A nasa bangaren, Tedros ya yabawa kasar Sin bisa yadda take ci gaba da tallafawa hukumar ta WHO.

Inda ya bayyana cewa, taimakawa hukumar WHO tamkar ceton tsarin gamayyar bangarori daban daban ne, jami'in WHO ya ce, a halin da ake ciki a yanzu ya kamata al'ummar kasa da kasa su karfafa goyon bayansu, kasancewar duniya tana cikin wani mawuyacin hali na yaki da annobar COVID-19 wacce ba ta la'akarin da kan iyakokin kasashe.

Ya ce ta hanyar yin hadin gwiwar yaki da annobar ne kadai al'ummar duniya za su samu nasarar dakile yaduwar annobar, idan ba'a yi hakan ba cutar za ta yi mummunan illa ga al'umma marasa galihu a kasa da kasa, kuma idan cutar ta ci gaba da daukar dogon lokaci, lamarin zai kara jefa rayuwar al'ummar duniya cikin matsanancin hali, kuma za'a samu hasarar rayuka masu yawan gaske.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China