Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya jagoranci taron shawo kan annoba da shirye-shiryen komawa bakin aiki
2020-04-08 21:13:20        cri
A yau Laraba ne shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jagoranci taron shawo kan annoba, da shirye-shiryen komawa bakin aiki na kasar Sin, a wani mataki na samar da sabbin tsare-tsare, na aiwatar da ka'idojin da ake amfani da su, wajen kandagarki da shawo kan cutar numfashi ta COVID-19, tare da kara fadada matakan komawa bakin aiki.

Taron na zaunannen kwamitin ofishin siyasa a kwamitin kolin JKS, ya nazarci halin da ake ciki game da cutar COVID-19, da kuma yanayin tattalin arzikin Sin a gida da waje. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China