Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Afirka za su kara dankon zumunci bisa hadin-gwiwar da suke yi a bangaren yakar cutar COVID-19
2020-04-17 20:44:25        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau Jumma'a cewa, yana da yakinin dankon zumunci tsakanin Sin da Afirka zai kara yaukaka bisa hadin-gwiwar da suke yi ta fannin yaki da cutar numfashi ta COVID-19.

Kwanan nan, ministan harkokin wajen tarayyar Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya jinjina dimbin nasarorin da kasar Sin ta samu wajen dakile yaduwar cutar, inda kuma ya yabawa managartan matakan da ta dauka wajen daidaita matsalolin da 'yan Afirka mazauna birnin Guangzhou suke fuskanta. Game da haka, Zhao Lijian ya ce, Sin da Afirka suna da makoma ta bai daya. A sa'ilin da Sin take kokarin dakile yaduwar cutar, 'yan uwa mutanen Afirka sun baiwa kasar babban taimako da goyon-baya.

Zhao ya ce, ganin yadda cutar COVID-19 ke kara yaduwa a kasashen Afirka, kasar Sin ta tura wasu tawagogin kwararrun likitoci guda biyu zuwa kasashen Habasha da Burkina Faso don taimaka musu yakar cutar. Kana, kasar za ta ci gaba da tura tawagogin kwararrun likitocinta zuwa kasashen Afirka daban-daban, da kara samar musu da kayan tallafin gaggawa. Akwai yakinin cewa, zumuncin dake tsakanin Sin da Afirka zai dada inganta, ta hanyar karfafa hadin-gwiwarsu wajen dakile yaduwar annobar.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China