Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na ci gaba da tallafawa kasashen Afirka wajen yaki da cutar COVID-19
2020-03-23 20:05:07        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce Sin za ta ci gaba da tallafawa kasashen Afirka, a yakin da kasashen ke yi da cutar numfashi ta COVID-19.

Geng Shuang wanda ya bayyana hakan, yayin taron manema labarai na yau Litinin a nan birnin Beijing, ya ce Sin na maida hankali matuka ga yanayin da ake ciki game da wannan cuta a Afirka, za ta kuma baiwa kasashen, da kungiyoyin nahiyar taimakamon kayayyakin bukata, ciki hadda sinadaran gano cutar, da kuma na ba da kariya.

A daya hannun kuma, jami'in ya ce Sin ta kira taro ta yanar gizo, domin musayar bayanai tsakanin kwararrun sassan biyu a fannin yaki da wannan annoba, ta kuma zaburar da masana a fannin, da suka shiga yakin da kasashen Afirkan ke yi da yaduwar cutar a kasashen nahiyar.

Geng ya kara da cewa, kayayyakin yaki da cutar na gaggawa da gwamnatin Sin ta samar domin tallafawa kasashen Afirka, za su isa nahiyar rukuni rukuni, yayin da a daya bangaren, Sin za ta ci gaba da tsarawa, da karfafar gwiwar kamfanoni da cibiyoyin da batun ya shafa, wajen shiga aikin yaki da wannan annoba yadda ya kamata a kasashen na Afirka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China