Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda masanan Amurka suka kirkiri labarin wai "Sin ta tilastawa musulmai 'yan Uygur aikin bauta" don bata sunan kasar Sin
2020-04-17 14:52:41        cri

A kwanakin baya, shafin intanet na Grayzone na Amurka ya wallafa wani bayanin da Ajit Singh ya rubuta, inda ya fayyace yadda masanan Amurka da hukumomin leken asiri na Amurka da sauran kasashen yammacin duniya da ma 'yan kasuwa masu sayar da makamai, suka samar da kudin taimako, suka kirkiri labarin wai Sin ta tilastawa musulmai 'yan Ugyur aikin bauta don bata sunan kasar Sin.

A cikin wannan bayanin da shafin intanet na Grayzone ya wallafa, an ce, wadannan labaran na shafa wa kasar Sin bakin fenti, abubuwa ne da Amurka, kungiyar EU, kungiyar NATO, da ma masana'antun kera makamai suka tsara tare da goyon bayansu. Idan an tsananta sabon yanayin cacar baki, to babu shakka za su samu dimbin muradu daga ciki.

Wannan bayani mai taken "Labarin 'aikin bauta' game da Sin daga gwamnatin Amurka da kungiyar NATO, da masana'antun kera makamai na da burin rura wutar yakin cacar baka" ya nuna cewa a wadannan kwanakin baya, kafofin watsa labarai sun yi ta zargin kasar Sin da tilastawa musulmai 'yan Ugyur aikin bauta. Hakika dai, an yada labaran bisa rahotanni uku da cibiyar nazarin manufofi da tsare-tsare ta kasar Australiya, cibiyar nazarin tsare-tsaren kasa da kasa ta Amurka, da ma Adrian Zenz, wani Kirista mai tsattsaran ra'ayi suka bayar.

A ranar 1 ga watan jiya, cibiyar nazarin manufofi da tsare-tsare ta Australiya ta bayar da wani bayani mai taken "Sayar da 'yan Ugyur: Mu ga yadda ake sake ilmantar da su, tilasta su wajen aikin bauta, da ma sanya musu ido a wajen jihar Xinjiang", wanda ya haddasa kafofin watsa labarai na yammacin duniya suka sake fara zargin kasar Sin.

Ma'aikatar tsaron kasar Astraliya ce ta samar da kudi ga wannan cibiyar, baya ga wadda ta samu daga masana'antun kera makamai na kasa da kasa kamar su Raytheon da Lockheed Martin. Wannan bayanin da cibiyar ta fitar a ran 1 ga watan Maris shi ma ya samu kudin taimako daga ma'aikatar harkokin waje da harkokin tarayya ta Birtaniya, da kuma hukumar leken asiri ta kasar.

A cikin wannan rahoton mai shafuka 56, babu shaidu ko kadan daga ma'aikatan da wai aka tilasta musu aikin bauta, sai dai ana amfani da shafukan biyu da ma labarin wata masana'anta don shaida yadda aka tilastawa musulmai aikin bauta.

Shafin Grayzone ya kuma fayyace cewa, wannan rahoton da cibiyar ta Australiya ta bayar ya waiwayi rahotanni biyun da ta taba bayarwa a baya, kuma daya daga cikinsu shi ne wani rahoton da Adrian Zenz, babban manazarcin asusun tunawa da wadanda suka mutu sakamakon Kwaminisanci ya rubuta, asusun kuma ya kasance wata kungiya mai rike da ra'ayi rikau, wanda gwamnatin Amurka ta kafa a shekarar 1983. Adrian Zenz, ya kuma taba sanar da cewa, yana gudanar da wani aikin da ke da nasaba da kasar Sin bisa umurnin Ubangiji.

Wannan rahoton na Adrian Zenz cike yake da shaci-fadi, kara gishiri, da ma maganar banza, shaida daya tak da ya yi amfani da ita shi ne wani labarin da wani shafin intanet na bidiyo mai tsattsauran ra'ayi ya bayar, wanda ya sha gayyatar masu kiyayyar Yahudawa, wadanda suka yi kira da yin Jihadi a kasar Sin ta hanyar daukar makamai.

Wannan rahoto maras tushe ko kadan ba a wallafa shi a shahararrun mujallun ilmi ba, sai dai an wallafa a wata mujallar da yake karkashin jagorancin NATO da masu leken asiri na Amurka.

Wani rahoto na daban da ya zargi kasar Sin da aiwatar da shirin tilastawa musulmai 'yan Ugyur aikin bauta, ya fito ne daga cibiyar nazarin tsare-tsaren kasa da kasa ta Amurka, inda ba a samar da wani sabon labari ba, sai dai dogaro da bayanin Adrian Zenz da wata hirar da aka yi a boye da wani wanda ba a so a fayyace sunansa ba, kuma wanda wai ake tsare shi don aikin bauta.

Wannan cibiyar kuwa ta kunshi masana masu ra'ayin nuna karfin soja bisa taimakon gwamnatin Amurka da wasu kawancenta na aikin soja. Ban da wannan kuma, cibiyar ta samu makudan kudaden daga dimbin masana'antun kera makamai, kamfanonin makamashi, da ma bankuna. (Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China