Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta jirkita gaskiya kan abun da ya faru a Guangdong
2020-04-13 19:57:40        cri
A game da zargin da Amurka ta yiwa kasar Sin na cewa wai ta nuna bambanci da wariya ga 'yan Afirka a yayin da take kokarin dakile yaduwar cutar COVID-19, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Zhao Lijian ya bayyana a yau Litinin cewa, yakar cutar COVID-19 na bukatar hadin kan kasa da kasa, amma ita Amurka ta jirkita gaskiya da rura wutar rikici, wannan abu ne da bai dace ba ko kadan.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya fadi cewa, a yayin da ake dakile yaduwar cutar COVID-19 a lardin Guangdong da sauran sassan kasar Sin, an nuna wariya da bambanci ga 'yan Afirka, kuma irin kyamar da kasar Sin ta nunawa baki 'yan kasashen waje abun takaici ne. Game da wannan furuci, Zhao Lijian ya shawarci Amurka ta maida hankalinta kan ayyukan kandagarkin yaduwar cutar a cikin kasarta, maimakon ta rika tsoma baki cikin dangantakar Sin da Afirka. Saboda a cewarsa, duk wani yunkurin Amurka na lalata dangantakar Sin da Afirka, ba zai yi nasara ba.

Zhao ya kuma jaddada cewa, kasar Sin ba ta taba sauya manufarta ta kulla dankon zumunci da kasashen Afirka ba, kana, babu wani abun da zai iya girgiza irin zumunci da kaunar da al'ummar kasashen Afirka suke nunawa kasar Sin.

Har wa yau, Zhao ya ce, gwamnatin kasar Sin na maida hankali sosai kan tabbatar da zaman lafiya da tsaron baki 'yan kasashen waje a yayin da take daukar matakan hana yaduwar cutar COVID-19, tana kuma nuna adalci ga daukacinsu dake kasar, da nuna adawa da duk wani yunkuri na nuna bambanci ga kowa da kowa.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China