Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya bayyana kudirin kasarsa na taimakawa Belgium da kayayyakin yaki da COVID-19
2020-04-02 20:28:40        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana kudirin kasarsa, na taimakawa kasar Belgium gwargwadon karfinta, don magance matsalar karancin kayayyakin kiwon lafiya da take fuskanta.

Xi, ya bayyana haka ne yau Alhamis, yayin zantawa da sarki Philippe na Belgium ta wayar tarho, yana mai cewa, a shirya kasarsa ta ke ta raba fasahohin kandagarki da hana yaduwar cutar COVID-19 da suka dace da kasar, da bunkasa alaka a fannin samar da alluran riga kafi da binciken maganin cutar gami da sauran fannoni.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China