Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rasha ta kafa sabuwar gwamnati
2020-01-22 13:02:37        cri
Jiya Talata, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanya hannu kan umurnin shugaba, inda ya tabbatar da tsarin hukumar gudanarwar harkokin kasa ta tarayyar Rasha, ya kuma nada mataimakin firaminista, da ministoci da wasu sabbin mambobin majalisar ministoci.

Fadar Kremlin ta gabatar da wannan umurnin shugaba a shafin intanet nasa. Ta ce, cikin sabuwar gwamnati ta kasar Rasha akwai mataimakin firaminista guda 9, ta kuma gabatar da jerin sunayen ministoci guda 21, kana kusan rabi daga cikinsu sabbin fuskoki ne, ciki har da ministan harkokin waje, ministan tsaron kasa, da ministan makamashi da dai sauransu.

Haka kuma, bisa labarin da aka samu daga shafin intanet na fadar Kremlin, an ce, a wannan rana, shugaba Putin ya gana da sabbin mambobin gwamnati, inda ya bayyana cewa, babban nauyin dake gaban sabuwar gwamnatin kasar, shi ne kyautata hidimar da za a samar wa al'ummomin kasa, da karfafa tsarin kasar Rasha, da kuma karfafa matsayin kasar Rasha cikin kasa da kasa.

A ranar 15 ga wata, shugaba Putin ya gabatar da takarda game da yanayin kasa ga majalisar dokokin kasa, sa'an nan, ya zartas da rokon firaminista Dmitry Medvedev kan murabus din sa daga gwamnati. Sa'an nan, a ranar 16 ga wata, shugaba Putin ya sa hannu kan umurnin shugaba, inda ya nada Mikhail Mishustin a matsayin sabon firaministan tarayyar kasar Rasha. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China