Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rasha ya kai farmaki kan masu fafutuka a yankin Idlib na kasar Sham
2020-02-21 10:41:55        cri
Cibiyar kasar Rasha mai shiga tsakanin bangarori daban-daban dake kasar Sham, ta ba da labari jiya Alhamis cewa, jirgin saman yaki na kasar samfuri Sukhoi-24, ya kai farmaki kan masu fafutuka a yankin Idlib dake kasar Sham, yankin da rikici ya fara sassautawa.

Kafofin yada labarai na Rasha sun ruwaito sanarwar da cibiyar ta bayar a wannan rana, inda ta ce, masu fafutukan sun kai hari sau da dama kan sojojin kasar Sham a wannan yanki, inda suka samun taimako daga sojojin kasar Turkiya, hakan ya sa 'yan tawayen su karya lagon dakarun gwamnatin kasar ta Sham.

Sanarwar ta kuma ce, bisa bukatar kasar Sham, Rasha ta tura jirgin saman yakinta zuwa kasar, don dakile wadannan masu fafutuka.(Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China