Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rasha na maida hankali sosai kan bikin murnar sabuwar shekara ta kasar Sin da CMG zai gabatar
2020-01-21 14:15:59        cri

An bada labari a yau Talata cewa, za a watsa gagarumin bikin murnar sabuwar shekara ta kasar Sin bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin ta shekarar 2020 a ranar 24 ga watan da muke ciki. Kafofin yada labarai da dama a kasar Rasha sun maida hankali sosai kan yadda aka shirya bikin. Kuma karon farko ne, birnin St.Petersburg zai watsa wannan biki na tsawon sa'o'i 4 kai tsaye ga dubun-dubatar masu kallo ta telibijin. Matakin kuma da ya fara jerin ayyukan murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin ta 2020 a St.Petersburg. Gwamnatin birnin da kuma karamin ofishin jakadancin Sin dake birnin sun yi hadin gwiwa wajen gabatar da wadannan ayyuka daga ranar 24 ga watan Janairu zuwa ranar 24 ga watan Fabrairu.

Bikin dai na da masu kallo mafi yawa a duniya, ciki hadda Sinawa biliyan 1.4, da kuma mutane 'yan asalin kasar Sin a duniya da 'yan kasashen ketare masu sha'awar al'adun kasar Sin. Shekarun baya-bayan nan, bikin ya fara jawo hankalin jama'ar kasar Rasha, abin da ya zama wata muhimmiyar kafa ce ta zurfafa zumuncin jama'ar kasashen biyu. (Mai fassarawa: Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China