Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin masu fama da COVID-19 na iya kaiwa miliyan daya nan da yan kwanaki in ji WHO
2020-04-02 12:04:37        cri

Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce mai yiwuwa nan da 'yan kwanaki, adadin mutanen da za su harbu da cutar numfashi ta COVID-19 a sassan duniya daban daban zai kai miliyan daya, kuma adadin wadanda cutar ke hallakawa na iya kaiwa 50,000.

Mr. Tedros ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, lokacin da yake bayani game da halin da ake ciki don gane da yaduwar wannan cuta. Ya ce "Yayin da aka shiga wata na 4 tun bayan bullar wannan cuta, na yi matukar damuwa game da saurin yaduwar ta a dukkanin sassan duniya".

Ya zuwa karfe 6 na yammacin jiya Laraba, bisa agogon tsakiyar Turai, annobar cutar COVID-19 ta hallaka mutane 40,777 a sassan duniya daban daban, yayin da adadin masu dauke da ita ya kai mutum 827,419 a kasashe da yankuna sama da 200.

Alkaluman hukumar WHO sun nuna cewa, a wajen kasar Sin, adadin masu fama da cutar ya haura zuwa mutum 744,781, yayin da ya zuwa yammacin ranar Laraba, adadin wadanda cutar ta hallaka suka kai mutum 37,456.

Mr. Tedros ya kara da cewa, baya ga kasashen dake da dubban masu fama da wannan cuta, su ma kasashen Afirka, da kasashen tsakiya da kudancin Amurka da cutar ba ta yadu sosai ba, akwai yiwuwar za su sha fama da tasirin ta a fannonin zamantakewa, da tattalin arziki da siyasa.

A daya bangaren kuma, Tedros yayi kira ga gwamnatoci, da su aiwatar da manufofin samar da tallafi, kamar na abinci da sauran kayan bukata na yau da kullum ga mabukata, musamman mutane masu rauni. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China