Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Adadin mutanen da suka kamu da COVID-19 a duniya ya zarce 900,000
2020-04-03 10:57:49        cri
Bisa alkaluman da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar da karfe 6:00 na yammacin ranar Alhamis, agogon CET ya nuna cewa, jimillar mutane 900,306 ne suka kamu da cutar COVID-19 a fadin duniya.

Adadin wadanda cutar ta hallaka ya karu zuwa 45,693.

A wajen kasar Sin, adadin mutanen da suka kamu da cutar ya kai 817,582, yayin da mutane 42,366 suka mutu ya zuwa yammacin ranar Alhamis.

A cewar hukumar WHO, a kasashen Italiya da Spaniya aka bada rahoton mutane 115,574 da 102,136 sun kamu da cutar.

A jawabin da babban daraktan hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya gabatar a ranar Alhamis yace, nan da kwana guda ko kwanaki biyu, adadin wadanda cutar COVID-19 zata kama a duniya zai zarce miliyan guda sannan mutanen da zasu mutu zai zarce 50,000. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China