Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Najeriya: Fasahar da Sin ta samu ita ce hanyar da kamata a yi a bi wajen nasarar dalike cutar COVID-19
2020-04-09 13:54:14        cri

Jiya Laraba, marubucin fitacciyar jarida a kasar Najeriya wato "The Daily Trust" John Chuks Azu ya rubuta sharhi mai taken "Yaya ake dalike annoba?", inda ya nuna yabo sosai kan yadda al'ummar kasar Sin suka hada kai, da dauki jerin managartan matakan shawo kan cutar numfashi ta COVID-19 cikin sauri, wadda ta ba da misali ga kasashe daban daban na yakar cutar, tare kuma da gabatar da managartan fasahohi, sharhin ya yi kira ga kasashen Afirka da su yi koyi da kasar Sin, don kara karfin nahiyar na kandagarkin cutar.

Ban da wannan, sharhin ya ce, a shekarar 2014, kasar Sin ta ba da tallafi ga nahiyar Afirka tare da hada kai wajen yaki da cutar Ebola, inda ta taimaka wa kasashen Afirka don kara karfinsu na dalike annoba, hakan ya aka kara wa kasar karfin kandagarki da shawo kan annoba da dabarun tinkarar annoba, don haka, fasahohin da kasar Sin ta samu wajen yakar annoba za su dace da halin da Afirka ke ciki. Ya kamata kasashe daban daban na Afirka su karfafa hadin gwiwa da Sin, da kara amfani da fasahohin da Sin da ta samu, don ganin bayan cutar nan da nan. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China