Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan masu kamuwa da cutar COVID-19 ya kai kimanin 12500 a nahiyar Afirka
2020-04-11 20:07:16        cri
Cibiyar shawo kan yaduwar cutattuka ta nahiyar Afirka ta gabatar da wasu alkaluma masu alaka da cutar COVId-19 a jiya Juma'a, inda ta ce yawan masu kamuwa da cutar ya kai 12,492. Cikinsu wasu 649 sun mutu, yayin da wasu 1,964 suka warke daga cutar. Zuwa yanzu cutar ta riga ta bazu zuwa kusan dukkan kasashen dake nahiyar Afirka, ban da Comoros da Lesotho. Sa'an nan alkaluman sun nuna cewa arewaci da yammacin Afirka sun fi jin radadin annobar, inda a yammacin nahiyar yawan wadanda suka kamu da cutar ya kai kusan 3,000.

A jiya Juma'a, an samu karin masu kamuwa da cutar COVID-19 38 a kasar Nijar, inda adadin masu cutar ya kai 448. Yayin da a Najeriya, aka samu karin wasu mutane 17 da suka kamu da cutar, wanda ya kawo adadin masu cutar a kasar zuwa 305. A kasar Ghana kuma, karin wasu mutane 65 aka tabbatar sun kamu da cutar, kana yawan masu cutar a kasar ya kai 378 yanzu. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China