Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Lardin Hubei zai dauki matakan samar da guraben ayyukan yi ga matalauta
2020-04-07 12:05:59        cri

Darektan ofishin yaki da fatara na lardin Hubei da ya yi fama da annobar COVID-19 Hu Chaowen, ya bayyana cewa, lardin zai bullo da wasu matakai don samar da guraben ayyukan yi ga matalauta, da rage tasirin radadin COVID-19 kan shirin rage talauci.

Karkashin wannan shiri, lardin zai yi hayar masu kare gandun daji 66,800 da samar da wasu ayyukan gatanci guda 50,000 ga wadanda ke fuskantar matsalar samun aiki yi.

Jami'in ya ce, kowane ma'aikaci dan cin rani, zai samu alawus na Yuan 200 kwatankwacin dala 28, kana wurin da suka dauke shi aiki, zai samu rangwame na daukar marasa aikin yi.

Haka kuma, za a yi amfani da matakai na harkokin kudi, don taimakawa matalauta jure wannan lokaci na wahala, ciki har da baiwa kananan sana'o'i da za su iya daukar manoma masu karamin karfi fiye da 10 aiki, rancen da zai kai Yuan miliyan 1 da za a biya kudin ruwa kadan.

Lardin Hubei dai na kan gaba wajen yakin da kasar Sin ta ke yi da COVID-19. Kuma ya zuwa ranar Lahadi, lardin ya yi rijistar mutane 67,803 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China