Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afrika ba za ta kasance wajen gwajin sabon rigakafin cutar COVID-19 ba
2020-04-07 11:06:59        cri
Darakta janar na hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana a jiya cewa, nahiyar Afrika ba za ta zama wajen gwajin kowanne irin riga kafin cutar COVID-19 ba.

Yayin wani jawabi da ya yi ta bidiyo, darakta janar din ya ce, za a bi dukkan ka'idojin gwajin rigakafi ko magani a ko ina a duniya bisa amfani da ka'ida iri guda a ko ina, ko a Turai ko Afrika ko sauran wurare.

Tedros Ghebreyesus, wanda da ya yi takaicin furucin wasu masana kimiyya wadanda suka ce a nahiyar Afrika za a gwada sabon rigakafin, ya ce dole ne a kawo karshen sauran ra'ayin mulkin mallaka dake akwai.

Ana zargin wasu likitocin kasar Faransa biyu da wariyar launin fata, bayan wata muhawarar da suka yi ta talabijin, da ta ba da shawarar aiwatar da gwajin a nahiyar Afrika, don ganin ko rigakafin cutar tarin fuka zai yi tasiri kan kwayar cutar Corona.

Tedros Ghebreyesus, ya bayyana cewa, ana sa ran nan gaba cikin wannan makon, WHO za ta sanar da wani shirin da zai gaggauta bincike da samar da rigakafin cutar COVID-19 da kuma hanyoyin rabawa yadda ya kamata.

A cewarsa, sama da kasashen 70 sun marawa hukumar baya kan gwajin rigakafin, domin gaggauta samar da ingantaccen magani. Kuma kimanin cibiyoyi da kamfanoni 20 na kokarin samar da shi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China