Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Najeriya: Ba mai yiyuwa ba ne Sin ta kera kwayar cutar COVID-19
2020-04-04 16:36:20        cri

Farfesan Femi Mimiko, masanin kimiyyar siyasa na jami'ar Obafemi Awolowo ta Nijeriya, ya wallafa wani sharhi mai taken "Shin kasar Sin ce ta kera kwayar cutar numfashi ta COVID-19?" a jaridar Newtelegraph ta jiya Juma'a, inda ya yi suka da babbar murya, kan jita-jitar da aka baza cewa kasar Sin ta kera kuma ta baza kwayar cutar COVID-19 domin ciyar da tattalin arzikinta gaba. Baya ga wannan, ya kuma bayyana tsarin shugabancin kasar Sin a matsayin tsarin gudanar da harkokin kasa mai karfi, wanda ba tabbatar da wadata a fadin kasar kadai ya yi ba, har ma da taka rawa wajen ci gaban duniya. Farfesa Femi Mimiko, ya kuma yi kira da a daina shafawa kasar Sin bakin fenti, tare kuma da kara karfafa hada kai tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a kai ga ganin bayan annobar nan da nan.

Sharhin ya ce, ya dace kasashen duniya su hada gwiwa a tsakaninsu domin samun dabarun dakile annobar tun da wuri, kada a ci gaba da bata lokaci kan mugun nufin bata sunan kasar Sin.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China