Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda suka mutu sanadin cutar COVID-19 a Afrika ya kai 313
2020-04-04 15:34:34        cri

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta nahiyar Afrika, ta ce adadin wadanda suka mutu sanadiyyar cutar COVID-19 a nahiyar ya kai 313, yayin da na wadanda aka tabbatar sun harbu ya kai 7,741.

Cikin sabon rahoton da ta fitar a yau, cibiyar Afrika CDC, ta ce an samu bullar cutar a kasashen nahiyar 50.

Ta kuma bayyana cewa, kasashen da cutar ta fi kamari sun hada da Afrika ta kudu mai mutane 1505 da suka harbu, sai Algeria mai mutane 986 yayin da Masar ke da mutane 985 da suka harbu.

Cibiyar ta kara da cewa, har ila yau a nahiyar, an sallami mutane 753 bayan sun warke daga cutar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China