Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jama'ar kasar Amurka suna goyon bayan kyaftin Crozier
2020-04-05 17:07:47        cri

 

Brett Crozier, shi ne tsohon kyaftin din babban jirgin ruwan yaki mai dauke da jiragen saman yaki na "USS Theodore Roosevelt CVN-71" na kasar Amurka, wanda ya taba rubuta wata wasika ga shugabannin sojojin ruwan kasar don sanar musu labarin barkewar cutar COVID-19 cikin jirginsa, tare da neman daukar wasu matakai don kare lafiyar sojojin dake cikin jirgin. Amma wannan wasikar ta sa aka sallame shi daga matsayin kyaftin a kwanakin baya. Sai dai yayin da ya bar jirgin wanda ya yi aiki cikinsa, a ranar 3 ga wata, sojoji sun taru sun yi masa ihu don jinjina masa, kan yadda ya yi kokarin kare lafiyarsu.

Jaridar San Francisco Chronicle ta kasar Amurka, ta ce kyaftin Crozier ya rubuta wannan wasikar neman taimako a ranar 30 ga watan da ya gabata, inda ya bayyana tsanantar yanayin fama da cutar COVID-19 a cikin jirgin ruwansa, da yadda aka kasa daukar matakai masu amfani sakamakon samun cunkuson mutane matuka, saboda haka ya bukaci shugabannin sojojin ruwan kasar Amurka da su ba da izini ga dukkan sojojin dake cikin jirgin ruwan da su sauka daga jirgin don a killace su, tare da yin jinyarsu.

Sai dai, wannan wasikar ba ta sa aka daidaita matsalar yadda ake bukata ba. An fara yin gwaje-gwajen kwayoyin cutar COVID-19 kan sojojin dake cikin jirgin ruwa, amma har yanzu ba a yarda dukkansu su sauka daga jirgin ba. A sa'i daya, an sallame Brett Crozier daga mukaminsa na kyaftin bisa dalilin cewa "ba shi da sanin ya kamata".

Wannan matakin ya janyo hankalin al'ummar kasar Amurka sosai, har ma kafofin watsa labarai da yawa sun wallafa bayanai don jinjinawa kyaftin Crozier, kan yadda ya yi watsi da mukaminsa don kare rayuka da lafiyar sojoji. A nasu bangaren, wasu jama'ar kasar su ma sun bayyana ra'ayoyinsu a shafukan sada zumunta, inda suka yabawa kyaftin Crozier, tare da nuna takaici ga gwamnatin kasar Amurka kan yadda ta kasa sauke nauyin dake bisa wuyanta. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China