![]() |
|
2020-03-31 10:22:18 cri |
Sanarwar da fadar White House ta Amurka ta fitar, ta ruwaito shugabannin sun tattauna kan yanayin da ake ciki da kokarin da ake yi na yakar cutar COVID-19. Sannan sun amince su yi aiki tare, karkashin kungiyar G20 domin cin nasarar yaki da cutar da kuma farfado da tattalin arzikin duniya.
Donald Trump da Vladimir Putin, sun kuma tabo batutuwan da suka shafi kasar Venezuela da kasuwar makamashi ta duniya. Inda suka amince da muhimmancin dake tattare da daidaita kasuwar makamashin ta duniya. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China