Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'ar Johns Hopkins: yawan masu fama da COVID-19 a Amurka ya zarce 100,000
2020-03-28 17:14:09        cri
Cibiyar nazarin tsarukan kimiyya da Injiniya ta jami'ar Johns Hopkins ta Amurka, ta ce adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a kasar ya zarce 100,000.

Cibiyar ta ce cutar ta fi kamari a jihar New York, inda ke da mutane 44,870 da suka harbu, sai jihar New Jersey dake da musu cutar 8,825, sai kuma jihar California da mutane 4,569 suka harbu.

A cewarta, baki daya a duniya, adadin wadanda suka kamu da cutar ya zarce 590,000 inda mutane kusan 27,000 suka rasa rayukansu. Sannan sama da mutane 130,000 sun warke daga cutar.

Yayin da annobar ke kawo tsaiko ga harkokin tattalin arziki da zamantakewa a Amurka, likitoci da ma'aikatan jinya da sauran ma'aikatan asibiti, na fama da karancin kayayyakin kiwon lafiya, ciki har da kayayyakin da za su kare kawunansu da kuma na'urorin taimakon numfashi ga marasa lafiya.

A jiya Juma'a ne shugaban kasar Donald Trump, ya bayyana cewa, ya ba kamfanin General Motors umarnin samar da na'urorin taimakon numfashin, karkashin dokar tsaro ta lokacin yaki, wadda ya yi amfani da ita a baya-bayan nan da nufin tunkarar cutar COVID-19. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China