Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnan jihar New York ya yabawa kasar Sin kan taimakon na'urar numfashi dubu 1 da ta aika musu
2020-04-05 16:08:15        cri

Kimanin na'urorin dake taimakawa numfashi 1,000 suka isa birnin New York a ranar Asabar wanda kasar Sin ta baiwa birnin gudunmawa, gwamnan jihar New York Andrew Cuomo ya tabbatar da hakan.

Duka a sakonsa na twita da kuma jawabin da ya yiwa manema labarai a safiyar ranar Asabar, Andrew ya godewa manyan attajiran 'yan kasuwar kasar Sin da suka hada da kamfanin Alibaba na Jack Ma da Joe Tsai, da gidauniyar Jack Ma da Joe da kuma gidauniyar Clara Tsai.

Kana ya godewa babban jami'in dake kula da karamin ofishin jakadancin kasar Sin a New York, Huang Ping, bisa taimakon da ya bayar har aka kai ga samun wannan taimako.

A cewar Andrew, taimakon ya zo a daidai lokacin da jihar ke tsananin bukata a kokarin dakile annobar COVID-19, wanda za su yi amfani da na'urorin taimakawa numfashin cikin kasa da mako guda. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China