Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump ya kafa dokar DPA don hana fitar da kayayyakin kiwon lafiya daga kasar a yayin da ake dakile annobar COVID-19
2020-04-05 15:30:33        cri

A ranar Juma'ar da ta gabata shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gabatar da yarjejeniyar ofishin shugaban kasa ta tsaron kayayyakin da ake kerawa a kasar wato (DPA) don hana fitar da kayayyakin kiwon lafiyar da ake kerawa a kasar zuwa kasashen ketare wato (PPE) yayin da ake fama da annobar cutar COVID-19.

A cewar yarjejeniyar, tilas ne a bayar da fifiko wajen amfanin cikin gida na kayayyakin kiwon lafiyar da ake kerawa, kuma a bayar da fifiko wajen samar da kayayyaki da suka hada da samfurin N95 da sauran na'urorin dake taimakawa numfashi, da takunkunmin rufe fuska, da safar hannu ta aikin lafiya domin kaucewa barazanar karancin kayayyakin a cikin kasar.

Sanarwar ta ce, sakataren tsaron cikin gida, ta hanyar jami'in hukumar agajin gaggawa na tarayyar kasar, za su ci gaba da tuntubar sakataren hukumar lafiyar kasar da bada himada ga jama'a, domin tabbatar da ganin an rarraba kayayyakin kiwon lafiyar zuwa wuraren da ya kamata karkashin kulawar bangarorin kula da lafiya da ayyukan hidimar jama'ar kasar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China