Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jam'iyyar Frelimo a Mozambique ta lashe babban zaben kasar
2019-10-28 10:40:15        cri
Hukumar zaben kasar ta Mozambique (CNE) ta sanar a ranar Lahadi cewa, dan takarar shugabancin kasar na jam'iyyar Frelimo mai mulki kana shugaban kasar mai ci, Filipe Nyusi, ya lashe babban zaben kasar inda zai yi wa'adin mulkinsa karo na biyu.

Shugaban hukumar zaben ta CNE Abdul Carimo, ya bayyana sakamakon zaben a wani taron da ya samu halartar wakilan jam'iyyun adawa, da masu sanya ido a zaben na ciki da wajen kasar.

CNE ta ayyana jam'iyyar Frelimo da dan takarar shugaban kasarta, Nyusi, cewa yana kan gaba da kashi 73% na kuri'un da aka jefa, kuma jam'iyyar ce take kan gaba a dukkan larduna 10 na kasar Mozambique, kana ita ce za ta lashe dukkan gwamnonin lardunan.

Dan takarar babbar jam'iyyar adawar kasar mai suna Renamo, Ossufo Momade, shi ne ya zo na biyu da kashi 21.88% na yawan kuri'un da aka kada, sai dan takarar jam'iyyar MDM wadda ita ce jam'iyya mafi girma ta uku a kasar Mozambique, Daviz Simango, ya samu kashi 4.38% na yawan kuri'un.

Sakamakon ya nuna cewa, jam'iyyar Frelimo tana da kujerun majalisa 184, jam'iyyar Renamo na da kujeru 60, yayin da MDM ke da kujeru 6 kacal.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China