Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An nada shugaban Ghana a matsayin gwarzon hukumomin kudi na AU
2020-02-13 11:30:03        cri
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya lashi takwabin taimakawa nahiyar Afirka, wajen ganin ta ci gajiyar hukumomin kudin dake nahiyar.

Shugaban ya bayyana haka ne yayin da aka nada shi a matsayin gwarzon hukumomin kudin kungiyar tarayyar Afrka ta AU. A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Talata, ta ruwaito Akufo-Addo na jaddada cewa, irin wadannan hukumomin kudi za su taimakawa bangaren kudin nahiyar daidaita matakan farfado da kuma samun ci gaban nahiyar.

Kasar Ghana ta yi imanin cewa, kafa hukomin kudi na Afirka, yana da muhimmanci wajen inganta matakan fadakar da al'umma game da yadda za a ci gajiyar albarkatu a nahiyar.

A matsayinsa na gwarzon shirin na AUFI, Akufo-Addo zai yi aiki da babban bankin Afirka (ACB) da asusun ba da lamuni na Afirka (AMF) da bankin zuba jari na Afirka (AIB) da kasuwar musayar hannayen jari ta Afirka (PASE).

Shugaba Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya kuma bayyana kudirinsa na yin aiki da shugabannin kasashen da aka kafa bankunan AMF, ACB da AIB a kasashensu wato Kamaru da Najeriya da kuma Libya.

Shirin na AUFI, daya ne daga cikin ayyukan shekaru 50 dake cikin ajandar raya nahiyar nan da shekarar 2063, ya kuma karkata ne wajen hade matakan bunkasa jin dadin jama'a da tattalin arzikin nahiyar Afirka. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China