Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan Ghana: kasuwanci ta yanar gizo wani muhimmin mataki ne na samar da aikin yi a Afrika
2019-12-26 11:20:36        cri

Ministar sadarwa na kasar Ghana Ursula Owusu-Ekuful, ta shaidawa manema labarai cewa, kasuwancin yanar gizo, na samarwa kasashen Afrika wata dama mai kyau, ta sauya salon tattalin arzikinsu, da samar da guraben aikin yi irin na fasaha.

Ta ce, rikici da dama dake faru a Afrika na da nasaba ne da talauci, da rashin daidaito, da nuna bambancin ra'ayi. Ta ce fasaha ta zama wata dama mai kyau ga matasan Afrika, don su samu aikin yi a fannoni daban-daban, ciki hadda kiwon lafiya, da ba da ilmi, da bunkasa aikin gona, da hukumomin kasuwanci da dai sauransu.

A cewarta, fasaha tamkar wata na'ura ce dake ingiza bunkasuwar yanar gizo, kuma za a iya samar da yanar gizo cikin sauki, kamar samun ruwa ko wutar lantarki.

Ta kara da cewa, bai kamata a nuna bambanci tsakanin matasa ba, saboda suna da hazaka kan kimiyya da fasaha, kuma idan ba su samu dama mai kyau ba, mai yiyuwa ne za su ta da rikici. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China