Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu sabbin mutane 12 da suka kamu da COVID-19 a Najeriya
2020-04-01 20:58:47        cri
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya, a yau Laraba ta tabbatar da sabbin mutane 12 da suka kamu da COVID-19, adadin da ya kai mutane 151 da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar dake yammacin Afirka.

Wata sanarwa da cibiyar ta fitar, ta ce cutar ta kuma halaka mutane biyu a kasar, kana an sallami mutane 9 daga asibiti bayan sun warke daga cutar.

Sabbin mutane 12 da suka kamu da cutar, sun fito daga jihohin Osun da Edo da Ekiti dake kudancin kasar.

Mutane 82 ne suka kamu da cutar a Lagos, cibiyar kasuwancin kasar, sai kuma Abuja, babban birnin kasar ta Najeriya, inda mutane 28 suka kamu da cutar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China