Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya jaddada muhimmancin gyaran fuska yayin rangadin aiki a lardin Zhejiang
2020-04-01 19:46:02        cri
A yau Laraba babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping ya bayyana bayan da ya saurari rahoton aikin lardin Zhejiang cewa, cinikayya tsakanin kasa da kasa ta gamu da mummunar matsala a sakamakon yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a wajen kasar Sin, haka kuma tattalin arzikin kasar Sin yana fuskantar sabon kalubale, a sa'i daya kuma ya samu sabuwar dama a bangarorin hanzartar ci gaban kimiyya da fasaha da kuma kyautatuwar sana'o'i. A bisa wannan yanayin, ya dace lardin Zhejiang na kasar ya mayar da hankali wajen yiwa muhimman fannoni gyaran fuska, ta yadda zai samar da sakamako da fasahohi ga sauran sassan fadin kasar ta Sin.

Lardin Zhejiang ya samu ci gaba cikin sauri tun bayan da aka fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga ketare a kasar, inda adadin GDP na lardin ya kai matsayi na hudu a kasar.

Shugaba Xi Jinping ya ziyarci biranen Ningbo da Huzhou da Hangzhou bi da bi tsakanin ranakun 29 ga watan Maris da 1 ga wata, inda ya gudanar da rangadin aiki mai zurfi a tashar ruwan teku da kamfanoni da kauyuka da wuraren kare muhallin halittu.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, duk da cewa ana fuskantar matsaloli, amma ya kamata a yi kokarin fito da sabuwar dama, a yayin da ake kokarin kandagardin annobar, ya dace a kara mai da hankali kan aikin dawo wa bakin aiki daga duk fannoni kuma cikin lumana.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China