2020-03-30 09:57:53 cri |
Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin koli na JKS Xi Jinping, ya ziyarci lardin Zhejiang a jiya Lahadi, domin duba yadda ma'aikata ke komawa bakin aiki da sake bude masana'antun lardin.
Shugaba Xi ya ziyarci yankin tashar ruwa ta Chuanshan, wadda ta hada tashoshin Ningbo da Zhoushan, kuma daya daga tashoshin ruwa na dakon kwantenoni mafi girma a duniya, wadda a shekarar 2019 aka yi amfani da ita, wajen dakon hajoji da suka kai Tan biliyan 1.12.
Kaza lika shugaba Xi ya kuma ziyarci yankin masana'antu na Ningbo, wanda ke samar da sassan injuna, da molin sarrafa hajoji daban daban. Rahotanni sun nuna cewa, dukkanin wadannan sassan na ci gaba da komawa bakin aiki cikin gaggawa. (Saminu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China