![]() |
|
2020-03-31 19:39:33 cri |
Xi ya bayyana haka ne jiya Litinin, yayin da ya ziyarci kauyen Yucun na garin Anji dake lardin Zhejiang a yankin gabashin kasar Sin. Ya ce, tsaunuka da ruwan dake wurin za su baiwa jama'a wata dama ta kara bunkasa tattalin arziki.
Xi ya ce, gina kasa ta zamani mai sigar garguzu, ya kunshi raya birane da aikin gona da yankunan karkara. Yana mai cewa, kasar Sin za ta dauki matakan da suka dace na farfado da yankunan karkara bayan gina al'umma mai matsakaicin ci gaba daga dukkan fannoni.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China