Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya jagoranci taro game da yaki da COVID-19 da tattalin arziki
2020-03-27 21:47:18        cri
Shugaban kasar Sin, kana babban sakataren kwamitin koli na JKS Xi Jinping, a yau Jumma'a ya jagoranci wani taron shugabanci, game da nazartar matakan yaki da cutar numfashi ta COVID-19, da kuma yanayin tattalin arziki.

Taron wanda ya hallara jami'an ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya tsara sabbin dabarun yaki da cutar COVID-19, da kuma matakan karfafa tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al'umma. An kuma tattauna game da rahotanni guda biyu, masu nasaba da yaki da talauci. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China