Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da suka kamu da COVID 19 a duniya ya kai dubu 750
2020-04-01 12:39:28        cri

Ya zuwa karfe 6 na daren jiya Talata agogon tsakiyar Turai, yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID 19 a duniya ya kai 754,948, kana yawan mamata a sanadin cutar ya kai 36,571, kuma cutar ta bulla a kasashe da yankuna 202.

Alkaluman da jami'ar The Johns Hopkins ta Amurka ya fitar na nuna cewa, ya zuwa karfe 5 na yammacin jiya Talata agogon wurin, yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar ya kai 181,099, yayin da yawan mutanen da suka mutu ya kai 3,606.

A Italiya kuma, kididdigar na nuna cewa, ya zuwa karfe 6 na daren jiya, yawan mutanen da suka kamu da cutar ya kai 105,792, yawan mamata kuma ya kai 12,428. Shugaban ofishin nazarin harkokin kiwon lafiya na Italiya Silvio Brusaferro ya ce, bisa rahoton nazarin karuwar masu kamuwa da cutar, an shiga wani yanayi na daidaitar yawan masu kamuwa da cutar a kasar.

Ban da wannan kuma, a kasar Faransa, yawan masu kamuwa da cutar ya kai 52,128, kana yawan mutanen da suka mutu ya kai 3,523. Karin mutane a Birtaniya da suka kamu da cutar ya kai 3,009, hakan ya sa jimillar mutanen da cutar ta harba a kasar kaiwa ga mutum 25,150, yayin da kuma cutar ta hallaka mutane 1789. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China