Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
The Atlantic: Donald Trump zai sha daci saboda katse huldar Amurka da Sin
2020-03-30 15:39:25        cri

Kwanan baya, mujallar The Atlantic ta Amurka ta wallafa wani bayani a kan shafin ta na yanar gizo, mai taken "Donald Trump zai sha daci saboda katse huldar Amurka da Sin" wanda farfesa Peter Beinart na jami'ar City University ta birnin New York ya gabatar.

Bayanin ya nuna cewa, a gabar mumunar cutar COVID-19, wasu 'yan siyasa da mashawarta na ganin cewa, kamata ya yi Amurka ta katse huldarta da kasar Sin. Amma, a hakika dai, darasin da wannan cuta ke baiwa Amurka ba katse alaka da daina hadin kai da kasar Sin ba, a maimakon haka, dole ne a farfado da hadin kan kasashen biyu kan kiwon lafiya, wanda gwamnatin Donald Trump ya rushe.

Ban da wannan kuma, bayanin ya ce, hadin kan kasashen biyu na da amfani sosai wajen yaki da cutar SARS a shekarar 2003, da kuma cutar H1N1 a shekarar 2009, har da ma cutar Ebola a shekarar 2014. Amma, a wannan shekara ta 2020, Donald Trump ya ba da shawarar rage rabin tallafi da Amurka take baiwa hukumar kiwon lafiya ta WHO, lokacin da ake fama da COVID-19 mai tsanani.

A halin yanzu dai, cutar ta dabaibaye duk fadin Amurka, kana hadin kan Sin da Amurka na da muhimmanci kwarai da gaske. Darektan cibiyar tsaron kiwo lafiya ta kwalejin kiwon lafiya dake jami'ar Johns Hopkins, Tom Inglesby ya nuna cewa, dangantakar kasashen biyu na da matukar muhimmanci wajen yakar cuta.

Dadin dadawa, bayanin ya ce, ra'ayoyin Trump na sabani da hakikanin gaskiya, saboda ganin yadda COVID-19 ke mahaukaciyar yaduwa. Wato a bangare daya, hadin kai na kasa da kasa zai iya kiyaye tsaron Amurkawa, saboda kowa da kowa na da alaka a cikin wannan duniya.

Wani bangare na daban shi ne, daidaito a tsakanin bangarori daban-daban kan ilmi da karfi ya canja. Yayin bullar cutar SARS a shekarar 2003, Amurka ita ce malamar kasar Sin. Amma, yanzu likitoci da masu kimiyya na Amurka na matukar bukatar fasaha, da kuma dabaru daga takwarorinsu na kasar Sin wajen cimma nasarar yakar cutar COVID-19 a birnin Wuhan. Bugu da kari, kamfanonin Sin zai zama sansanin samar da makaman yakar cutar a duniya.(Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China