Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rage kudin likitanci ya sa karuwar mutanen dake kamuwa da COVID-19 cikin sauri a Amurka
2020-03-29 17:12:17        cri
Ya zuwa yammacin ranar 28 ga wata da misalin karfe 6 da minti 2, agogon gabashin kasar Amurka, gaba daya adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 ya kai 121117, daga cikinsu, wadanda suka rasa rayuka sun kai 2010, ko wace rana sabbin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar sun zarta 20000.

To ko menen dalilin da ya sa adadin yake karuwa cikin saurin haka a Amurka? Kwanakin baya wasu kafofin watsa labarai na kasar sun bayyana cewa, akwai dalilai da dama kamar haka:

Na farko, an wargaza tsarin hana yaduwar cututtuka na kasar. A ranar 13 ga wata, tsohuwar babbar jami'ar ofishin tsaron lafiyar kasa da kasa ta hukumar kiyaye tsaron Amurka Beth Cameron ta wallafa wani rahoto a jaridar Washington Post, inda ta bayyana cewa, shugaban kasar Donald Trump ya wargaza ofishin a watan Mayun shekarar 2018, mamban hukumar kiyaye tsaron kasar mai kula da aikin hana yaduwar cututtuka a kasar Timothy Ziemer ya yi murabus ba zato ba tsamani, lamarin da ya janwo gaza dakile annobar a kan lokaci.

Na biyu, gwamnatin kasar ta rage kudin da aka kebe kan aikin kiwon lafiyar kasar, lamarin da ya sa hukumomin da abin ya shafa na kasar sun gamu da wahala yayin gudanar da aiki.

Labaran da aka gabatar a tashar intanet ta Foreign Policy ta Amurka sun nuna cewa, an fara rage kudin lafiyar kasar ne tun daga shekarar 2018, har adadin ya kai dala biliyan 15, kana ta rage kasafin kudin hukumomin CDC da NSC da DHS da kuma HHS, har ta kawar da asusun daidaita rikici mai tsanani da yawansa ya kai dala miliyan 30.

Na uku, Trump bai dauki matakai masu karfi ba yayin da kasar take kokarin dakile annobar, lamarin da ya sa kasar tana fama da matsalar karancin kayayyakin likitanci.

Tashar talabijin ta CNN ta Amurka ta nuna cewa, yayin da kasar take gamuwa da rikicin bazuwar annobar COVID-19, Trump bai dauki matakan da suka dace ba, kana yayin da masana lafiyar jama'ar kasar suka yi gargadin cewa, barazanar cutar za ta ci gaba har tsawon watanni, Trump shi ma ya bayyana cewa, za a farfado tattalin arzikin kasar kafin karshen watan da muke ciki, sabon sakamakon nazarin da jami'ar Washington ta yi ya nuna cewa, duk da cewa gwamnatin Amurka ta dauki matakai masu karfi nan take, sai dai adadin mutanen da za su mutu sakamakon annobar zai karu kafin watan Yuli mai zuwa.

Yanzu asibitocin birnin New York suna cikin mawuyacin yanayi saboda karancin na'urorin taimakawa numfashi, haka kuma sauran jihohin kasar kamar su Washington da California da Louisiana su ma za su shiga irin wannan yanayi.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China