Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin masu fama da cutar COVID-19 ya kai kusan dubu 700 a sassan kasa da kasa
2020-03-31 14:08:14        cri

Bisa kididdigar da hukumar kiwon lafiyar kasa da kasa ta WHO ta fidda, an ce, ya zuwa karfe 6 na yammacin jiya Litinin, bisa agogon tsakiyar Turai, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a sasssan duniya ya kai 697,244, yayin da cutar ta hallaka mutane 33,257. Yanzu haka dai, an samu yaduwar cutar a kasashe da yankuna 203.

Kuma bisa kididdigar da jami'ar Johns Hopkins ta kasar Amurka ta fidda, an ce, ya zuwa karfe 6 da rabi na yammacin jiya Litinin, agogon gabashin Amurka, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar ya kai 160,020, yayin da mutane 2,953 suka rasa rayukansu.

A sa'i daya kuma, yazuwa karfe 6 na yammacin jiya Litinin, gaba daya akwai mutane 101,739 da suka kamu da cutar a kasar Italiya, adadin da ya karu da 4,050 idan aka kwatanta da na ranar Lahadi da ta gabata, kuma mutane 11,591 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar.

Ya zuwa karfe 9 na ranar 30 ga wata, adadin mutane da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar Burtaniya, ya kai 22,141, adadin da ya karu da mutum 2,619 cikin yini guda. Kuma, ya zuwa karfe 5 na yammacin ranar 29 ga wata, mutane 1,408 sun rasu sakamakon kamuwa da cutar, adadin da ya karu da mutum 180 cikin yini guda.

A kasar Faransa ma, adadin mutanen da suka kamu da cutar ya karu zuwa 44,550 a ranar 30 ga wata, wanda ya karu da mutum 4,376 cikin yini guda. Kuma gaba daya mutane 3,024 sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar, adadin da ya karu da mutum 418 cikin sa'oi 24, wanda shi ne adadi mafi yawa da kasar ta samu tun bayan barkewar cutar. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China