Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rashin yin bincike a kan lokaci ne ya haddasa kasawar Amurka wajen dakile yaduwar COVID-19
2020-03-31 13:57:13        cri

A halin yanzu, adadin mutanen da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Amurka ya kasance mafi yawa a duniya baki daya. Dangane da wannan batu, jaridar The New York Times ta fidda wani sharhi, inda ta bayyana cewa, hukumomin gwamnatin tarayyar kasar Amurka da dama sun yanke hukunci maras dacewa, kuma ba su dauki matakai a kan lokaci ba, lamarin da ya sa cutar numfashi ta COVID-19 ta yi ta yaduwa a duk fadin kasar ta Amurka, gwamnatin kasar ta bata lokaci na kusan wata guda wajen aikin dakile yaduwar annobar a cikin gida.

Kuma bisa binciken da jaridar The New York Times ta yi, an ce, a farkon watan Fabrairu, kasar Amurka ba ta fara bincike kan cutar numfashi ta COVID-19 a duk fadin kasar Amurka ba, inda ta kuma gamu da babbar matsala kan aikin. An gano cewa, kayan binciken da shugaban cibiyar rigakafi da hana yaduwar cututtuka ta kasar Amurka Robert Redfield ya ba da jagoranci wajen kerawa yana da matsala, ko da yake Robert Redfield ya yi alkawari cewa, zai warware matsalar cikin sauri, amma, ya kasa warware matsalar bayan makwanni da dama.

A wannan lokaci, hukumar sa'ido kan abinci da magungunan kasar Amurka ta fidda wata sabuwar manufa, wadda ta haddasa karin matsaloli wajen gudanar da bincike kan cutar numfashi ta COVID-19, lamarin da ya sa, Amurka ta kasa dakile yaduwar annobar a cikin gida yadda ya kamata.

Ko da yake, ana ci gaba da zargin cibiyar rigakafi da hana yaduwar cutuka da hukumar sa'ido kan abinci da magunguna a kasar Amurka, amma ma'aikar kula da harkokin kiwon lafiya da bada hidima ga jama'a ta kasar Amurka, wadda take bada jagoranci ga wadannan hukumomin biyu, ba ta fidda matakan da suka dace ba wajen warware matsalar.

Dangane da wannan lamari, tsohon shugaban cibiyar rigakafi da hana yaduwar cutuka ta kasar Amurka Thomas Frieden ya bayyana cewa, a karshe dai, mun samu matakai masu amfani wajen gudanar da bincike kan cutar, amma sun makara, lamarin da ya nuna kasawar gwamnatin kasar kan wannan aiki.

A nata bangare kuma, tsohuwar shugabar hukumar sa'ido kan abinci da magungunan kasar Amurka Margaret Hamburg ta ce, wannan matsala ta haddasa matukar karuwar adadin masu kamuwa da cutar a kasar Amurka. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China