Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsohuwar babbar jami'ar gwamnatin Amurka ta yi suka ga gwamnatin Trump saboda jan kafa wajen dakile cutar COVID-19
2020-03-22 20:47:01        cri

Jaridar Independent ta kasar Burtaniya ta rawaito tsohuwar mai baiwa shugaban kasar Amurka shawara kan harkokin tsaro, madam Susan Rice, ta yi suka ga shugaba Donald Trump saboda sakacin da ya yi wajen shawo kan annobar cutar COVID-19, duk da cewa an riga an yi gargadi.

Susan Rice ta yi wannan furuci ne a yayin da take zantawa da CNN. Rice ta taka rawar gani a lokacin da gwamnatin Obama ke shawo kan cutar Ebola, sannan kuma kafin jami'an gwamnatin Trump su kama aiki, tawagar Rice ta taba yi musu gargadin yiwuwar sake barkewar cutuka masu yaduwa.

A shekarar 2018, gwamnatin Trump ta bada umarnin wargaza ofishin kula da lafiya da tsaron jama'a na duniya, abun da ake tsammanin daya ne daga cikin dalilan da suka sa gwamnatin Amurka ta yi jinkirin wajen maida martani kan barkewar cutar COVID-19.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China