Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Financial Times ta wallafa sharhi dake nuna rashin tsarin Amurka na tunkarar annoba
2020-03-27 16:51:07        cri

A ranar 26 ga wata agogon Amurka ne, jaridar Financial Times ta Burtaniya ta wallafa wani sharhin Edita mai taken "Rashin halin ko'ina kula da fadar White House ta nuna kan COVID-19"

Sharhin ya bayyana cewa, koda yake tawagar masanan fadar White House kan yaki da COVID-19, sun yi imanin cewa, sai bayan watan Mayu ne cutar za ta kai kololuwarta yaduwarta a Amurka, Shugaba Trump yana fatan cewa, ayyuka za su dawo a Amurka a ranar 12 ga watan Afrilu, yana mai cewa, an zabi wannan rana ce, saboda, "Rane ce mai muhimmanci." Masana lafiya sun kuma ba da shawarar zama a gida don rage yaduwar cutar, amma shugaba Trump, yana son miliyoyin Amurkawa su koma bakin aiki. Irin wannan mataki na shugaba Trump, zai kara jefa kasar cikin hadarin yaduwar cutar zagaye na biyu, da ma koma bayan tattalin arziki a nan gaba.

Jaridar ta kara da cewa, barkewar cuta, ta kara fito da gazawar Amurka cikin gomman shekaru na tafiyar da shugabancin kasar, tattalin arziki da kula da jin dadin jama'a. A wannan makon ne, hukumar lafiya ta duniya ta yi gargadin cewa, a matsayinta na kasar mafi karfin tattalin arziki a duniya, Amurka za ta iya zama sabuwar cibiyar da cutar ta fi kamari. Don haka, sharhin ya ce, ya kamata gwamnatin Trump, ta amsa laifin da ta aikata kan wannan batau. Fadar White House ba ta da tsari na zahiri a kasa da bayanai game da hana yaduwar wannan cuta. Shugaban da kansa, ya taba furta kalaman masana lafiya mabambanta yayin taron manema labarai. Sakamakon haka,kamfanoni a wasu fannonin da abin ya shafa suna iya yankewa kansu shawara kan matakan da suka dace su dauka. Haka kuma, Amurka ta bar kananan hukumomi da gwamnatocin jiohin kasar, da su tsara manufofinsu na yaki da wannan annoba. Matakan da a lokuta da dama suka haifar da takarar neman kayayyakin kiwon lafiya.

A karshe, sharhin jaridar ya bayyana cewa, a mataki na kasa, ya kamata shugaba Trump, ya martaba shawarar masana kimiya da kwararru a fannin tattalin arziki, ciki har da wadanda ba su shafi Wall Street ba, su rika sanar da jama'a bayanai a kai a kai. Wadannan matakai, suna da muhimmanci ga harkar kiwon lafiya, kasuwanci da daidaita ladan 'yan kwadago a lokacin annoba. Amma abin bakin ciki, Trump bai san da haka ba. Wannan babban hadari ne ba ma kawai ga kasar Amurka ba, har ma ga duniya baki daya. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China