Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
New York Times: Trump yana neman shafawa Sin kashin kaji don kawar da hankalin Amurkawa
2020-03-23 11:05:07        cri

Jaridar New York Times ta wallafa wani sharhi a ranar 20 ga wata mai taken "Kar ku bar Trump ya gudu", tana mai cewa, yadda Trump ya canja sunan kwayar cutar COVID-19 zuwa "kwayar cutar kasar Sin", wani yunkuri ne na kawar da tunanin jama'a don ya boye bazawarsa wajen tunkarar cutar.

A cewar sharhin, halayyar Trump game da wannan annoba, ta sha bamban da yadda ya saba yi, kuma dabararsa game da cutar akwai rudarwa, abin da ke nuna cewa, gwamnatin Trump tana kokarin canja tunanin jama'a don ceto kasuwar hannayen jari tare da mayar da martani kan sokar da jama'a ke yi mata.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China