Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya dace kasashen duniya su dauki matakai tare cikin gaggawa
2020-03-29 16:23:36        cri
A yammacin ranar 26 ga wata, agogon birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron kolin musamman na G20 da aka shirya kan batun yadda za a dakile annobar numfashi ta COVID-19, inda Xi ya yi kira cewa, a wannan muhimmin lokaci, ya dace mu hada kai mu dauki matakai tare cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba.

A daidai wannan lokaci mai muhimmanci na dakile annobar da take bazuwa cikin sauri a fadin duniya, a karo na farko ne shugabannin kasashen da suka fi saurin ci gaban tattalin arziki da shugabannin hukumomin kasa da kasa sun tattauna kan batun kai tsaye ta kafar bidiyo, shi ne kuma karo na farko da shugabannin G20 suka kira taron ta kafar bidiyo a tarihi.

Yayin taron, shugaba Xi da sauran shugabannin kasashe mambobin kungiyar G20 sun yi shawarwari kan yadda za a yaki annobar COVID-19, wadda ke kara tsanani a halin yanzu, inda Xi ya gabatar da dabaru guda hudu dake kumshe da: hana yaduwar cutar a duniya, da gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, da samar da goyon baya ga hukumomin kasa da kasa, da kara karfafa sulhuntawa kan manufofin tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasa da kasa.

Hakika kafin taron, shugaba Xi ya riga ya tattauna ta wayar tarho da shugabannin kasashe ko hukumomin kasa da kasa da yawansu ya kai 22 har sau 26, a ciki, ya tattauna da shugabannin kasashe mambobin G20 har sau 14.

Kasar Sin tana samarwa kasashen duniya da dama tallafin da suke bukata gwagwadon karfinta, kawo yanzu gwamnatin kasar Sin ta sanar da cewa, ta riga ta samarwa kasashe 89, da hukumar lafiya ta duniya da kungiyar tarayyar kasashen Afirka da sauran hukumomin kasa da kasa tallafin kayayyakin likitanci cikin gaggawa, kamar su maganin tantance kwayar cutar, da takunkumin rufe fuska, kana kasar Sin ta gabatar da tallafin kudi dalar Amurka miliyan 20 ga hukumar lafiya ta duniya domin gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa yayin da suke kokarin ganin bayan annobar, ban da haka kananan gwamnatocin biranen kasar Sin, da kamfanonin kasar, da kungiyoyi masu zaman kansu na kasar su ma sun samar da taimako ga kasashen da annobar ta fi kamari. Ana iya cewa, taimakon da kasar Sin take samarwa ga sauran kasashen duniya, babban aikin jin kai mafi mihimmanci ne take gudanarwa tun bayan da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin a shekarar 1949.

Rahotanni sun nuna cewa, a daidai wannan lokaci, ana kara fahimtar ma'anar tunanin kyakkyawar makomar bil adama da kasar Sin ta gabatar.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China