Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan siyasa na Amurka na ci gaba da mai da hankali a kan shafa wa wasu kashin kaji duk da hali mai matukar wahala da kasar su ke ciki
2020-03-26 20:41:04        cri
"Shawarar da ma'aikatar harkokin waje ta Amurka ta bayar(a gun taron ministocin harkokin waje na G7) ta tabo batu mai tada kura, ba zai yiwu ba a yarda da irin wannan mataki na alakanta cutar da wata kasa da kuma yayata irin bayanin."

 

 

A jiya Laraba, kafar CNN a rahoton ta, ta ruwaito kalaman wani jami'in diplomasiyya na Turai, dangane da yadda shawarar sakataren harkokin waje na Amurka Mike Pompeo ta saka kalmar "cutar Wuhan" cikin hadaddiyar sanarwar taron ministocin harkokin waje na G7 ta samu rashin amincewa daga mahalarta taron, har ma matakin ya sa taron ya kasa kaiwa ga fitar da hadaddiyar sanarwa.

 

 

Ya zuwa yanzu, yawan mutanen da suka harbu da cutar COVID-19 a kasar Amurka ya kusan kai dubu 70, yayin da karuwar masu kamuwa da cutar ta kai sama da dubu 10 a cikin kwanaki uku a jere.

A ranar 24 ga wata, kakakin hukumar lafiya ta duniya(WHO) ya yi hasashen cewa, mai yiwu ne Amurka za ta zamanto kasar da cutar ta fi kamari a duniya. Duk da cewa a kwanan nan, shugaban kasar ya yi shelar daina ambaton cutar da "cutar kasar Sin", amma in mun yi la'akari da furucin Mr. Pompeo, za mu gane cewa, har yanzu wasu 'yan siyasa na kasar ba su daina kiyayya, da kuma raini ga kasar Sin ba, kuma suna ci gaba da neman shafa wa kasar Sin kashin kaji, don kawar da hankalin al'umma kan yadda suka yi sakaci da aikinsu wajen dakile cutar.

Kafofin yada labarai na Amurka sun labarta cewa, har zuwa yanzu, da wuya talakawan Amurka su samu damar gwajin cutar a kansu, ga shi kuma matsalolin karancin gadajen marasa lafiya da kayayyakin jinya sun kara tsananta. Rush Doshi, babban manazarci a cibiyar nazari ta Brookings ta Amurka ya yi suka da cewa, gardama a kan ko ya kamata a yi wa cutar COVID-19 lakabin "cutar Wuhan", ya lalata hadaddiyar sanarwar taron ministocin harkokin waje na G7, a yayin da cutar ke addabar kasashen duniya, lalle abin takaici ne, wadda kuma ta sabawa aikin shugabanci.

Cuta abokiyar gaba ce ga 'yan Adam baki daya, kuma kasa da kasa na bukatar su zama tsintsiya madaurinki guda. A yau Alhamis ne aka kaddamar da taron musamman na shugabannin kungiyar G20 kan yaki da cutar COVID-19. Tuni kuma kasar Sin ta bayyana fatanta, na ganin ta hada kai da kasashen kungiyar, don tabbatar da nasarar taron. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China