Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masar ta jaddada aniyar tallafawa shirin zaman lafiyar Sudan ta kudu
2020-03-26 11:17:08        cri

Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya jaddada aniyar kasarsa na tallafawa yarjejeniyar baya bayan nan ta kafa gwamnatin hadin kan kasa a Sudan ta kudu domin cimma nasarar wanzar da zaman lafiya mai dorewa a kasar.

Tsokacin na al-Sisi ya zo ne a lokacin da ya amsa kiran wayar tarho daga shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir, wanda ya bayyana farin cikinsa game da taimakon da kasar Masar ke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiyar kasarsa, kakakin shugaban kasar Masar Bassam Rady shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

A watan Fabrairu, Kiir da tsohon mataimakin shugaban kasar wanda daga bisani ya zama madugun 'yan adawar kasar Riek Machar, sun sanar da amincewa da kafa gwamnatin hadin kan kasar domin kawo karshen yakin basasa da kasar Sudan ta kudu ta tsunduma. An kuma sake rantsar da Machar a matsayin mataimakin shugaban kasar na farko, baya ga wasu mataimakan shugaban kasar uku.

A cewar sanarwar, shugaban kasar Masar ya jaddada bukatar dukkan bangarorin kasar Sudan ta kudu su ci gaba da yin aiki tare domin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar kasar.

A nasa bangaren, Kiir ya jaddada aniyar Sudan ta kudu wajen ci gaba da yin hadin gwiwa da kasar Masar a dukkan fannoni a nan gaba. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China